Ghana za ta gabatar da kuduri ga MDD don ayyana cinikin bayi a matsayin laifi

Kasar Ghana za ta gabatar da kuduri ga Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a watan Maris na 2026 don ayyana cinikin bayi na Afirka a

Kasar Ghana za ta gabatar da kuduri ga Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a watan Maris na 2026 don ayyana cinikin bayi na Afirka a matsayin “laifi mafi girma ga bil’adama.

Shugaban Ghana John Dramani Mahama ne ya bayyana hakan a karshen taron shekara-shekara na 39 na Tarayyar Afirka (AU) a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Shugaban Ghana ya dauki wannan matakin a matsayin mataki na farko zuwa ga amincewa da girman cinikin bayi na transatlantic.

Ya bayyana cewa shawarwari da abokan hulda da dama, da kuma goyon bayan Tarayyar Afirka, zai karfafa wannan shirin har ya yi nasara.

” Cinikin bayi na transatlantic shi ne mafi girman rashin adalci kuma mafi girman laifi akan bil’adama,” in ji John Dramani Mahama.

A cewar Shugaban Ghana, kudurin da za a gabatar wa kasashe membobin Majalisar Dinkin Duniya zai dauki siffar sanarwa kan bautar da ‘yan Afirka da kuma cin zarafin ‘yan Afirka ta hanyar launin fata, wadanda ake dauka a matsayin manyan laifukan cin zarafin bil’adama.

“A yanzu, burinmu shine mu gabatar da kudurin ga Majalisar, don ba wa duniya damar gane cewa wannan ya faru kuma babu wani rashin adalci da ya fi girma a kan bil’adama a cikin kwanan nan ko tarihin duniya fiye da cinikin bayi,” in ji shugaban kasar Ghana.

A cewar UNESCO, wannan cinikin ya shafi ‘yan Afirka miliyan 15 zuwa 20 wadanda aka kama aka kuma tura su da karfin tsiya zuwa Amurka da Caribbean.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted