Masu fasaha na ƙasashen duniya sun goyi bayan jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Albaniya, suna jaddada adawarsu da matsin lamba ga waɗanda ke fallasa kisan kare dangi na Gaza
Fitattun mutane sama da 100 daga duniyar fasaha da nishaɗi sun sanya hannu kan wata buɗaɗɗiyar wasiƙa don goyon bayan ƙwararriyar masaniyar kare haƙƙin ɗan adam na Majalisar Dinkin Duniya Francesca Albanese, wacce ke fuskantar mummunan matsin lamba da nuna kahon zuka gami da yin kira da a yi mata murabus bayan da ta yi suka ga kisan kare dangi da aka yi a Gaza, tana mai bayyana shi a matsayin “abin kunya ga wannan zamani.”
Wasiƙar, wadda ƙungiyar masu fasaha ta Falasɗinu ta shirya, ta haɗa da fitattun mutane kamar su Mark Ruffalo da Javier Bardem, marubuciyar da ta lashe kyautar Nobel Annie Ernaux, da mawaƙiya Annie Lennox, da kuma Rosa Salazar, Asia Argento, Yorgos Lanthimos, Kawthar Ben Hania, Resident, da Nan Goldin.
Masu sanya hannu kan takardar sun tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Albanese a matsayin mai kare hakkin dan adam da kuma ‘yancin al’ummar Falasdinu na wanzuwa, suna masu jaddada cewa: “Akwai mutane marasa adadi a cikinsu a kowane sako na duniya waɗanda suke ƙin nuna karfi kan raunanne da ake zalunta.”