Iran Za Ta Koyawa Shugaban Amurka Darasi Mai Daci Idan Yayi Gigin Kai Mata hari

babban kwamandan dakarun sojin kasar iran Majo janaral Abdulrahim musavi ya gargadin shugaban Amurka Donald Trumph game da duk wani yunkurin kai wa iran Hari

babban kwamandan dakarun sojin kasar iran Majo janaral Abdulrahim musavi ya gargadin shugaban Amurka Donald Trumph game da duk wani yunkurin kai wa iran Hari domin za ta koya masa darasi mai daci inda ya kuskura ya kai harin.

Yace tabbas Trump zai fahimci cewa lallai ya shiga cikin wata sarkakiya da zai koya masa darasi mafi muni ,domin samakamo ne da zai sa ba zai kara yin wata barazana ba a duniya, yace barazanar yaki da trumph yake yi duk shaci fadi ce idan da gaske ne me yasa yake magana kan tattaunawa .

wannan gargadin da kwamandan yayi ya zo ne yan watanni bayan da shugaban Amurka Donald Trumph yake ci gaba da yin barazanar daukar matakin soji kan kasar Iran, trump ya aike da dakarun soji zuwa yankin da hakan ya kara sanya damuwa na yiyuwar kai harin soji, ko a ranar jumaa ma pentagon ta sanar da aike da da karin jiragen yaki zuwa yankin , kuma za su sake aikewa da dubban dakaru da sauran makamai da nauraron kakkabo makamai masu linzami

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted