Declassified:  Fiye Da Sojojin Birtaniya 2000 Ne Su Ka Yi Yaki A Cikin Sojojin “Isra’ila” A Gaza

Shafin kasar “Declassified” wanda yake fito da bayanan sirri na hukuma a Biraniya ya ce, da akwai dubban sojoji daga kasashe masu yawa daga ciki

Shafin kasar “Declassified” wanda yake fito da bayanan sirri na hukuma a Biraniya ya ce, da akwai dubban sojoji daga kasashe masu yawa daga ciki hard aga Birtaniya da su ka shiga cikin sojojin “Isra’ila” wajen yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi.

Bayanin ya ce; Daga Birtaniya kadai sojoji 2000 ne su ka hade da na Haramtacciyar Kasar Isra’ila” daga watan Maris na 2025.

Adadin sojojin kasashen waje da su ka fito daga kasashe mabanbanta da su ka taya “Isra’ila” kisan kiyashi sun kai 50,000,mafi yawancinsu sun fito ne daga kasashen Amurka, Rasha, Ukiraniya Faransa da kuma Jamus.

Gabanin wannan fallasar, majiyoyin Birtaniya suna cewa adadin ‘yan kasar da su ka je Isra’ila su ka taya ta kisan kiyashi akan al’ummar falasdinu ba su wuce 54 ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted