Iran: Tauraron Dan Adam Mai Suna ‘Jame-Jam 1’ Ya Isa Kilomita Dubu 36 Daga Doron Kasa

Tauraron dan adama na hukumar gidan radiyo da talabijan na JMI, wanda kuma zai watsa shirye-shiryen gidajen radio da talabijan na hukumar, ya isa tazarar

Tauraron dan adama na hukumar gidan radiyo da talabijan na JMI, wanda kuma zai watsa shirye-shiryen gidajen radio da talabijan na hukumar, ya isa tazarar kolimita dubu 36 daga doron kasa.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto kamfanin dillancin labaran –Faza wa nujum-na JMI yan sa’o’in da suka gabata ne tauraron Jame-Jam ta isa falakin da zai tsaya wanda yake da tazarar kilomita 36,000 daga doron kasar.

Labarin ya bayyana cewa tauraron wanda aka sanya masa suna IRAN DBS, hukumar gidajen radio talabijan na kasar Iran ya dade yana gina shi, daga karshe ya kai ga natija.  

Labarin ya kara da cewa an yi amfani da kumbo mafi karfi a duniya mallakin kasar Rasha wanda kuma yake kasar Kazakistan mai kuma suna Proton-M  don isar da wannan tauraron dan adam zuwa wani wuri wanda masana ilmin sararin samaniya suke kira GEO.

Ana saran idan wannan tauraron dan adama ya fara aiki zai wasta sauti da kuma hotunan tashoshin talabijan na hukumar IRIB.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted