Shugaban Iran Ya Kaddamar Da Kamfanoni 1,376 A Fadin Kasar A Wannan Talata

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya kaddamar da kamfanini manya manya da kanan wadanda gwamnatinsa ta samar ko ta kammala ko kuma ta farfado da

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya kaddamar da kamfanini manya manya da kanan wadanda gwamnatinsa ta samar ko ta kammala ko kuma ta farfado da su.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban ya kaddamar da sabbin kamfanoni har 868, sannan wasu 508 kuma kamfanoni ne da suka rushe sannan aka sake tada su. Shugaban yayi haka ne a dai dai lokacinda kasar take cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin musulunci wanda ya sami nasara tun shekara 1979. Wasu kamfanonin an dade da farasu amma ba’a karasasu ba sai a wannan shekarar mai karewa.

Shugaban ya kaddamar da dukkan wadannan kamfanonin ta taron hotunan bidiyo a nan Tehran. Ya kuma godewa ma’aikatar raya kamfanoni da ma’adinai da kuma kasuwanci wadanda suka taimaka wajen ganin an kammala wadan nan ayukan.

Labarin ya kara da cewa an kashe tuman triliyon 776 don kaiwa ga wannan gagarumin nasarar, wacce zata samar da ayyukan yi gay an kasar, ya kuma bunkasa tattalin arzikin kasar duk tare da matsalolin da makiya suke samarwa a kan wannan tafarkin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted