Tsohon ministan tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi dirar mikiya kan fira ministan Yahudawan Sahayoniyya Netanyahu kuma ya zarge shi da ‘ƙarya’
Musayar zarge-zarge tsakanin tsohon ministan tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun ci gaba da ƙaruwa sakamakon gazawar da ta faru kafin harin “Ambaliyar Al-Aqsa.” Wannan zargi na baya-bayan nan ya zo ne a ranar Asabar lokacin da tsohon ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya bayyana fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a matsayin “maƙaryaci.”
Gallant ya yi tsokaci kan hujjojin da Netanyahu ya bayyana game da gazawar da ta faru kafin harin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023.
A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta 12 ta Isra’ila, Gallant ya ce game da waɗannan hujjojin: “Suna da fira minista mai ƙarya… Yayin da sojojin Isra’ila ke mutuwa, ya zaɓi ya daba musu wuka a baya.” Ya ɗauki sakin takardun a matsayin wani ɓangare na yunƙurin mayar da zargi da tayar da hankali ga shugabannin rundunar tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro da na siyasa da kuma sojoji da dama a yankin suka amince cewa harin na ranar 7 ga watan Oktoba ya kunshi gazawar tsaro da leken asiri da soja da kuma siyasa.