Rahotannin da suke fitowa sun ce wasu samarin Falasdinawa 3 sun jikkata a harin da ‘yan share wuri zauna su ka kai a yankin ” al-Makhbah”.
A can kudu masu gabashin Nabulus kuwa an yi taho mu gama ne a tsakanin falasdinawa mazaunan “Ra’asul-Ayn” dake kudu masu gabashin Qasrah, da kuma ‘yan share zauna.
A cikin watannin bayan nan ‘yan share wuri zauna suna tsananta kai hare-hare akan Falasdinawa da kona musu dukiya da ta hada dabbobi da kuma motocinsu.
A yankin Gaza kuwa, Falasdinawa 2 Ne Su Ka Yi Shahada A cikin Sa’oin Kadan Da Su Ka Gabata
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa, Falasdinawa 2 sun yi shahada a cikin sa’oi kadan da su ka gabata, sai kuma wasu mutane 25 da su ka jikkata.
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta ce; har ya zuwa yanzu da akwai wani adadi mai yawa na shahidai dake karkashin baraguwai da sojojin mamaya su ka rusa akan mutanen da suke a raye. Rashin kayan aiki da su ka dace ne ke hana a fito da gawawwakin shahidan kamar yadda ma’aikatar ta kiwon lafiya ta sanar.
Daga lokacin da aka sanar da cewa, an tsagaita wutar yaki a ranar 11 ga watan Oktoba na 2025 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kashe Flaadinawa da sun kai 576 ta kuma jikkata wasu da sun kai 1,543.
Jumillar falasdinawan da su ka yi shahada kuwa tun daga 7 ga Oktoba na 2023, zuwa yanzu sun kai 72m027, yayin da adadin wadanda su ka jikkata ya kai 171,651.
Sai dai wadannan alkalumman suna sauyawa a kowane lokaci bisa la’akari da yadda sojojin mamayar suke ci gaba da kai hare-hare a yankin na Gaza.