Baqa’i: Tattaunawar Iran Da Amurka Na Birnin Muscat Ya Yi Kyau Tare Da Jaddada Aniyar Ci Gaba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran da Amurka sun amince su ci gaba da tattaunawa Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran da Amurka sun amince su ci gaba da tattaunawa

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya ce: Tattaunawar da aka yi tsakanin Iran da Amurka a birnin Muscat ta kawo ƙarshe cikin kyakkyawan yanayi inda ɓangarorin biyu suka amince su ci gaba da tattaunawa.

Baqa’i ya rubuta a shafinsa na Twitter a ƙarshen wani sabon zagaye na tattaunawa da Amurka a ranar Juma’a: “Tattaunawar da aka yi tsakanin Iran da Amurka a Muscat ta ƙare cikin kyakkyawan yanayi inda ɓangarorin biyu suka amince su ci gaba da tattaunawa.”

Ɓangarorin biyu, yayin da suke bayyana ra’ayoyinsu da buƙatunsu, sun amince su yanke shawara game da zagaye na gaba na tattaunawa da kasashensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted