Kakakin sojin kasar iran birgediya janar mohammad Akrami nia yayi gargadin cewa iran ta shirya tsaf domin kare kanta daga duk wata barazana, ya ce damuwar Amurka ya karu saboda saukin da iran ta samu na isa zuwa ya sansanoninta dake yankin
bayanan da birgediya Ganar Akrami nia ya yi wata alamace dake nuna irin shirin da sojojin iran suke ciki,adaida lokacin dake ci gaba da samun tankiya tsakaninta da Amurka, kuma ya bayyana karin samun jiragen sama mara matuki fiye da 1000 da kuma tsarin tsaro na sararin samaniya da aka samu.
hakazalika ya kara da cewa iran ashirye take ta fuskanci duk wani yanayi ko na diflomasiya ko na soja , kuma sanarwar ta zama gargadi na kai tsaye ga sojojin Amurka a yankin, yana mai jaddada cewa iran tana da ikon kai hari kan sansanonita a duk fadin yankin, da haka zai yi tasiri sosai a yankin da kuma tattaunawar diflomasiya ta kasa da kasa.
daga karshe yayi gargadin cewa duk wani yaki to zai shafi dukkan yankin ne da kuma dukkan sansanoni Amurka dake yakin da yankunan da aka mamaye na tekun fasha da tekun oman saboda samun isa zuwa ga sansanin Amurka yana da sauki sosai yanzu a gare mu.