Bincike ya tabbatar da cewa: Yawan mutanen Gaza ya ragu da 254,000 saboda yaki a yankin
Wani bincike mai inganci da jaridar The Guardian ta Birtaniya ta buga ya kammala da cewa yawan mutanen yankin Gaza ya ragu da kimanin mutane 254,000, ko kuma kashi 10.6%, idan aka kwatanta da kiyasin kafin fara yaki a ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023.
Binciken da aka gudanar, wanda Kwalejin Geneva ta Duniya kan Dokokin Jin Kai da Hakkokin Dan Adam ta gudanar, ya ruwaito cewa yara 18,592 da kuma mata kimanin 12,400 aka kashe a Gaza kafin karshen shekara ta 2025.
Binciken ya nuna cewa: Duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a watan Oktoban shekara ta 2025, an kashe daruruwan Falasdinawa tun daga lokacin.
Ya bayyana cewa dokar kasa da kasa, wacce ke da nufin takaita tasirin yaki, ta kai wani matsayi na wargajewa sakamakon yaduwar laifukan yaki da kuma kusan rashin hukunta wadanda suka aikata laifi.
Tun lokacin da aka fara yakin a Gaza, Falasdinawa 71,000 aka kashe tare da jikkata sama da 171,000.
A cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, sojojin mamayar Isra’ila sun kashe Falasdinawa 509 tare da raunata 1,405 tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 11 ga Oktoba, 2015.
Kwanaki da suka gabata, sojojin Isra’ila sun amince a karon farko – bayan fiye da shekaru biyu da suka musanta – sahihancin bayanan da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta buga, wanda ya bayyana cewa na’urar kashe mutane ta Isra’ila ta yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da 70,000 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2013.