Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya bada sanarwan cewa shirin tattaunawa da kasar Amurka kan shirinta na makamashin Nukliya yana kankama, duk tare da shirin yakin da kasar ta yi na tunkarar duk wani hari a kan kasar.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Dr Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa, shirin tattaunawar yana kankama, duk tare da shirin yaki da kasar ta yi na tunkarar Amurka.
Kafin haka dai Washington tace dole ne Iran ta dakatar da dukkan shirinta na makamashin Nukliya, ta takaita tazarar makamanta masu linzami da kuma daina shishigi a cikin al-amuran kasashen yankin.
Tehran tace makamanta na linzami baa bin tattaunawa bane kwata-kwata don sune ginshikin tsaron kasar, sannan zata tattaunawa da Amurka dangane da shirinta na makamshin Nukliya ne kawai idan washinton ta yarda Iran ta tache makamashin yunarium a cikin gida.