Mataimakin ministan al’adu da koyarwar musulunci na Iran ya ce baje kolin shekara-shekara na al’kur’ani na shekarar bana wanda shi ne karo na 33, zai dauki taken; Iran A Karkashin Kariyar Al’kur’ani Mai Girma.”
Hujjatul-Islam Hamid Riza Arbab Sulaimi wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron kwamitin tsara baje kolin, ya bayyana cewa; yana da kyau ya zamana an bayyana taken bajen kolin na bana.
Haka nan kuma ya ce, an zabi wannan taken ne saboda ya zamana dukkanin jawaban da za a gudanar a yi su a karkashinsa,bisa la’akari da halin da ake ciki a wannan lokacin.
A kowace shekara a farkon watan Ramadana mai alfarma ana bude baje kolin alkur’ani mai girma wanda yake kunsar littatafai da ayyukan fasaha masu alaka da al’kur’ani mai girma da kamfanoni mabanbanta suke kawo ba. Haka nan kuma a tsawon lokacin baje kolin na al’kur’ani mai girma ana gabatar da jawabai a matakai mabanbanta domin koyar da ma’anonin da suke cikin alkur’ani ga manya da kuma kananan yara da matasa.
Mahukunta kan gabatar da abincin buda-baki ga dubban mahalarta baje kolin wanda yakan dauki rabin watan Azumi ana yinsa, wasu lokacin har zuwa karshe. Ana kuma fara bude dakunan baje kolin ne da rana har zuwa tsakar dare na dararen Ramadan mai alfarma.