A yau Laraba ne aka yi jana’izar shahidan da su ka kwanta dama a sanadiyyar hargitsin bayan nan wanda Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka ingiza ‘yan ta’adda da hanyar ba su makamai da na’urorin leken asiri.
Dubun daubatar mutane ne su ka fito yi wa shahidan rakiya zuwa makwancinsu na karshe a nan birnin Tehran da aka farad aga bakin jami’ar Tehran.
Jana’izar ta samu halartar manyan jami’an gwamnati da al’ummar gari da su ka fito daga kowane bangare na na al’umma.
Adadin shahidan da aka yi jana’izarsu a yau sun kai 100 da masu yi musu rakiya su ka rika bayar da taken yin tir da Amurka da kuma ‘yan sahayoniya.