Gwamnatin Qatar ta ce tana tattaunawa da mahukuntan Iran da na Amurka domin kauce jefa yankin a cikin wani sabon rikici.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ya sanar cewa Doha tana tuntubar bangarori daban-daban domin rage rikicin yankin da kuma warware takaddamar da ke tsakanin Iran da Amurka.
Majed Al-Ansari, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar, ya bayyana a wata hira da tashar Al Jazeera, cewa: “Muna cikin bangarorin da ke tuntubar sauran masu ruwa da tsaki don rage tashin hankali a yankin da kuma warware takaddamar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka.”
Ya kara da cewa: “Diflomasiyya hanya ce mai kyau don warware takaddamar da ke faruwa a yankin.”
Al-Ansari ya ci gaba da cewa: “Muna dogara da wannan hanyar diflomasiyya a cikin hadin gwiwarmu da abokan huldarmu da makwabtanmu.”
Wadannan kalamai sun zo ne yayin da yankin ke fuskantar yanayi mai tsarkakiya saboda tsoma bakin Amurka da barazanar da take yi wa al’ummomin yankin, musamman kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.