An Daure Shugaban Yan Adawa Na Kasar Baharain Na Tsawon Wata 6 Saboda Sukan Isra’ila

Shugaban yan adawa na kasar Bahrain Ebrahim Sharif zai yi zaman gidan yari na tsawon watanni 6 saboda caccakar HKI da yayi game da ayyukan

Shugaban yan adawa na kasar Bahrain Ebrahim Sharif zai yi zaman gidan yari na tsawon watanni 6 saboda caccakar HKI da yayi game da ayyukan ta’adanci da take yi, tun a watan nuwamba yake tsare a gidan yari  saboda zargin shi da yada labarin karya a kafofin sada zumunta inda ya soki kasashen larabawa da shuwagabanninsu.

A ranar Alhamis wata kotu a kasar baharain ta yanke wa fitattce dan adawa na kasar hukumci daurin watanni 6 a gidan yari  kuma zai biya tarar dinari 200 dai dai da dalar Amurka 530.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Luu-Luu  sharif ya bayyana cewa kasashen larabawa sun kasa taimakawa alummar falasdinu , kuma ya soki shuwagabannin kasashen larabawa da suke mayar da hulda da HKI sannu a hankali.

Kasar Baharai tana daga cikin kasashen larabawa da suka mayar da hulda da HKI tun  a shekara ta 202o a wani bangare na yarjejeniyar Abraham da shugaban Amurka Donald trumph ya gabatar tun a zangon farko na mulkinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted