Rahotanni sun bayyana cewa dubban iraniyawa ne suka taru a birnin Qazvin domin bayyana adawar su ga masu zanga-zangar da suka fito da makamai suna kisa da kone dukiyoyin gwamnati da na alumma dake samun goyon bayan isra’ila, inda suka rika rera taken yin Allah wadai da Isra’ila da Amurka.
Yanayin yadda ake gudanar da zanga-zangar yana kara zama abin damuwa ga alummar iran musamman yadda kasashen waje suke kara yin tasiri da kuma tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar, sai dai yanayin hadin kai da aka samu a lokacin zanga-zangar ya nuna yadda alummar iran ke fafutukar kare hakkokinsu.
Haka zalika masu zanga-zangar sun nuna matsayarsu kan wanda ke kawo cikas ga tsaron kasar, wani da ya halarci zanga-zangar da yake Magana kan Amurka da Isra’ila ya fadi cewa bamu yar da ku kawo cikas ga zaman lafiyar kasarmu ba, kuma dukkan ku kuna samun goyon baya da tallafi daga hukumomin leken asirin gwamnatin sahyuniya da Mossad da Amurka ne, don haka zamu tsaya tsayin daka don kare kasarmu daga duk wata barazana ,