Kungiyar kasashen musulmin ta sanar da cewa za ya yi taron ne a yau Asabar saboda a fitar da matsaya ta kasashen musulmi akan yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta dauki yankin Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
Taron na yau Asabar a birnin Jiddah na kasar Saudiyya zai mayar da hankali ne akan muhimman abubuwan da suke faruwa ne a cikin Somaliya,bayan da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta furta amincewa da yankin a matsayin kasa mai ‘yanci da cin gashin kai.
Matakin na ‘yan sahayoniya dai ya fuskanci suka daga kasashen larabawa da na musulmi wanda manufarsa tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen larabawa da kuma sake killace su daga yankin da ake kira zirin Afirka.
Somaliland dai wani yanki ne na kasar Somalia, wanda ya shelanta ballewa da ayyana kansa a matsayin ‘yantacciyar kasa, sai dai babu wata kasa a duniya da ta amince da hakan, in ba Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yanzu ba.