An Gudanar Da Zanga zangar Nuna Goyon Bayan Alummar Falasdinu A Koriya Ta Kudu.

A kasar koriya ta kudu dubun dubatan Alummar kasar ne suka fito a babba birnin koriya ta kudu a yau Asabar domin nuna goyon bayansu

A kasar koriya ta kudu dubun dubatan Alummar kasar ne suka fito a babba birnin koriya ta kudu a yau Asabar domin nuna goyon bayansu ga alummar falasdinu da kuma yin tir da siyasar Isra’ila kuma sun bukaci a aike da taimakon jin kai cikin gaggawa ga alummar Gaza.

Kamfanin dillancin labarai na Irna ya nakalto cewa adaidai lokacin da ake cikin mawuyacin hali a yankin Gaza da hana bude mashigar rafah da isra’ila tayi domin shigar da kayan agaji, wanda hakan ya sabama matakin farko na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma da trumpa ya bullo da ita, wannan yasa dubban alummar birnin Suul suka fito zanga-zanga nuna goyon bayan falasdinu da bukatar bude hanya a isar da kayan agaji garesu.

Daga karshe mahukumta a yankin Gaza sun bayyana irin mawuyacin halin da aka shiga fiye da kowanne lokaci a yankin Gaza saboda rufe mashigar rafah da aka yi, da kuma hana shigar da kayan agaji, don haka sun yi kira da kasashen da suka shiga tsakani suka lamince wajen dakatar da bude wuta da su matsa lamba kan Isra’ila da ta dakatar da keta yajejeniyar cikn gaggawa kafin ta rushe baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted