Ministan Tattalin Arziki Na Lebanon Ya Jaddada Wajabcin Bunkasa Harkokin Kasuwanci Da Iran

Ministan tattalin arziki na Lebanon Amir al-Bisat  ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakunci ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci a birnin

Ministan tattalin arziki na Lebanon Amir al-Bisat  ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakunci ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci a birnin Beirut,wanda kuma ya sami halartar babban jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran din akan tattalin arziki  da kasuwanci.

A nashi gefen ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci ya yi Ishara da alaka mai tsawo ta fuskar kasuwanci da ttatalin arziki a tsakanin Iran da Lebanon, sannan ya bayyana cewa a halin yanzu Iran din a shirye take ta bunkasa wannan alakar.

Daga cikin fagagen da bangarorin biyu su ka tattauna yin aiki tare a tsakaninsu da akwai aikin gona, yawon bude ido da ayyukan al’adu da kuma rage yawan kudaden fito ta a cikin kasuwanci.

A wani labarin mai alaka da Ziyara zuwa kasar Lebanon, Abbas Arakci ya ziyarci hubbaren  shahid Sayyid Hassan Nasrallah domin girmama shi da kuma shahidan gwgawarmaya. Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada ci gaba da nuna goyon bayan Iran ga gwgawarmaya da manufofin da ta ginu a kansa.

Arakci ya ce; A madadin gwamnati da al’ummar Iran ina yin jinjina ga dukanin masu tafiya a tafarkin gwgawarmaya da kare gaskiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted