Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Isa Birnin Beirut Na Kasar Lebanon Don Ziyarar Aiki

Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya isa birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ziyar yan kwanaki, inda ake saran zai gana da

Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya isa birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ziyar yan kwanaki, inda ake saran zai gana da jami’an gwamnatin kasar musamman tokwaransa na kasar ta Lebanon kan al-amura da dama.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fada a jiya Laraba bayan taron majalisar ministocin kasar kan cewa ziyarar da zai kai kasar Lebanon a wannan karon ta karfafa dangantaka mai tsawo dake tsakanin kasashen biyu.

Ministan ya ce wasu yan kasuwa da jami’an tattalin arziki na gwamnati zasu yi masa rakiya.

Kafin haka dai Aragchi ya gayya tokwaransa na kasar Lebanon Youssef Rajji  wanda yace masa ba zai iya zuwa Iran a halin yanzu ba, kuma sai dai hadu a wata kasa ta 3. Amma Aragchi ya fada masa cewa shi zai zo don su tattauna kan al-amura da dama daga cikin akwai batun kwance damarar makaman kungiyar Hizbullah ta kasar, wanda HKI da Amurka suke takurawa gwamnatin kasar ta yi haka don ta basu damar damar mamayar kasar.

HKI dai ta bayyana a fila kan cewa zata mamaye kasar Lebanon ta kuma hada ta da HKI don fadada kasar. Kuma kasar Lebanon na daga cikin kasashen da take son ta mamaye amma kungiyar hizbullah wacce take samun goyon bayan JMI ta hana hakan faruwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted