An Bude Ofishin Jakadancin Falasdinu A Hukumance A Birnin Landan Na Kasar Burtania

An bude ofishin jakadancin kasar Falasdinu a hukumance a birnin London na kasar Burtania a ranar Litinin, bayan da gwamnatin kasar ta amince da samuwar

An bude ofishin jakadancin kasar Falasdinu a hukumance a birnin London na kasar Burtania a ranar Litinin, bayan da gwamnatin kasar ta amince da samuwar kasar Falasdinu a cikin watan satumban da ya gabata.

Jaridar ‘The Nation’ ta kasar Amurka ta nakalto jakadan kasar Falasdinu a kasar Burtania Husam Zomlot yana cewa bude ofishin jakadancin Palasdinu a birnin London wani babban ci gaba a gwagwarmayar falasdinawa na kimani karni guda.

A wani karamin buki wanda aka gudanar a wajen ofishin jakadancin Zomlot ya yaye labulen da aka rufe rubutun ofishin jakadancin, a gaban wasu jami’an gwamnatin kasar Burtania, Falasdinawa mazauna burtania, da jami’an kungiyar Common wealth, da jami’an jakadancin wasu kasashen Larabawa da musulmi.

Ya kuma kara da cewa daga yau Falasdinawa suna da gida a kasar Burtania nesa da gida, kuma wannan zai kara kyautata dangantakar kasar Falasdinu da kasar Burtania. Har’ila yau sharer fage ne na samun kasar Falasdinu mai cikekken yenci nan ba da dadewa ba.

A cikin watan Satumban shekarar da ta gabata ce gwamnatin kasar Burtania ta yanke shawarar amincewa da samuwar kasar Falasdinu sannan sauran wasu kasashen yamma suka bi sawunta, daga cikinsu har da kasashen Autralia da Canada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted