Shugaban Kasar Columbia: Trump Yana Son Yi Wa Yankin “Latin” Mulkin Mallaka

Shugaban kasar Columbia Gustav Petro ya bayyana cewa; Abinda shugaban kasar Amurka Donald Trump  yake son yi, shi ne shimfida wani sabon mulkin mallaka a

Shugaban kasar Columbia Gustav Petro ya bayyana cewa; Abinda shugaban kasar Amurka Donald Trump  yake son yi, shi ne shimfida wani sabon mulkin mallaka a cikin yankin Latin da mayar da shi karkashin Amurka.

Petro ya wallafa a shafinsa na X a jiya Talata cewa: Siyasar wajen Amurka ta ginu ne akan mulkin mallaka a cikin kasahsen Latin. Haka nan kuma ya ce; Trump yana amfani ne da hanyoyin da Adolf Hitler na Jamus ya yi amfani da su, wajen cimma wannan manufa, domin shi ne abinda akidar siyasar “Monroe’ take nufi.

Haka nan kuma shugaban na kasar Columbia ya ce; Siyasar Trump tana cin karo da dokokin kasa da kasa, wacce take nufin ware wani yanki da mayar da shi ;hakkin wata kasa; da ita ce akidar da Hitler ya yi aiki da ita, da a karshe ta kai ga afkuwar yakin duniya na farko da na biyu.

Da kuma yake Magana akan garkuwa da shugaban kasar Venezuela da Amurka ta yi, shugaba Petro ya ce a shirye yake ya dauki makami domin fuskantar kasar Amurka.

Donald Trump dai ya sha yi wa kasashen yankin Latin barazana da su ka hada da Columbia. A bayan nan ya fada wa shugaba Gustav Petro cewa; Kwanakinsa akan Mulki ba za su dade ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted