Shugaban Colombia Gustavo Petro, ya sanar cewa zai “sake daukar makamai” don mayar da martani ga barazanar da takwaransa na Amurka, Donald Trump, ke yi, a daidai lokacin da ake ta samun tashe-tashen hankula tsakanin kasashen biyu bayan harin da sojojin Amurka suka kai a Venezuela.
“Na rantse ba zan sake taba makami ba bayan yarjejeniyar zaman lafiya ta 1989, amma saboda kare kasa ta, zan sake daukar makamai,” in ji shugaban Colombia a shaffin X.
Donald Trump ya bayyana a ranar Lahadi a cikin jirgin Air Force One cewa wani abu a Colombia makamancin wanda aka gudanar a Venezuela zai iya faruwa.
Ya kuma zargi Gustavo Petro da safarar miyagun kwayoyi zuwa Amurka.
” Donald Trump ya tabbatar cewa Cuba “ta shirya faɗuwa” bayan kame Nicolás Maduro.