Masu zanga-zanga sun kwarara kan titunan biranen Amurka suna allawadai da aikin sojen da gwamnatin shugaba Trump ta ke yi a kasar Venezuela da kuma da kuma kama shugaba Madoro da matarsa Cilia Flores.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga-zanga a mafi yawan biranen Amurka suna nuna damuwarsu da wani yakin da gwamnatinTrump ta shiga a kasar Venezuela wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa, da kuma bayyana hakan keta hurumin kasar Venezuela ne.
A birnin Philidelphia nab akin ruwa, mazu zanga-zanga sun yi tattaki daga City Hall zuwa cibiyar daukan sojojin Amurka da ke birnin suna daga murya da wasu kalmomi masu yin allawadai da yaki da kuma kama shugaba madoro. Wasu suna cewa majalisa ce yakamata da amince da dukkan yakin da shugaban kasa zai shiga.
Kama shugaba Madoro da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya a birnin NewsYork da sunan yana safarar kwayoyi ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Sannan a birnin NewYork kuma Zohran Mamdani magajin garin birnin yana cewa aikata laifin yaki ne kai farmaki kan kasar Venezuela.