Rahotanni sun nuna cewa jagoran juyin musulunci a iran Ayatullah Imam khamna’I ya bayyana cewa yanayin yadda farashin dala yake tashi a kasar ba lamari ne da aka saba da shi ba, domin akwai hannun makiya wanda sanyawa farashin ya zama haka.
Jagoran yayi wannan bayani ne a lokacin da yake ganawa da iyalan shahidai da suka hada da iyalan shahid janar qasim Sulaimani a yau Asabar wanda sojojin Amurka suka kashe a wani hari da suka kai a birnin bagadaza na kasar Iraqi a ranar 3 ga watan janerun shekara ta 2020
Da yake bayani kan zanga-zangar baya bayan nan da aka yi a kasar da ta fara daga babbar kasuwar Tehran a makon jiya jagoran yace yan kasuwar Tehran suna daga cikin mutanen da suke da cikakkiyar biyayya ga juyin juya halin musulunci don haka babu wanda zai iya karawa da tsarin musulunci da sunan yan kasuwa.
Ayatullahi Khamena’I yace shugaban kasa da manyan jami’an gwamnati suna ta kokari wajen samar da mafita, yace karuwar kudaden kasahen waje ba bisa ka’ida ba, abu ne da ya sabawa doka kuma makiya suna da hannu a ciki, kuma dole ne a dakatar da shi.
Haka zalika jagoran yayi gargadi game da fakewa da korafin tattalin arziki daga masu adawa, yana me cewa abin da yafi muhimmanci shi ne wasu mutane ne suka fusata wadanda suka zama sojojin haya na makiya suna tsayawa a bayan kasuwanni suna rera takin kin musulunci , da kuma kin jamhuriyar musulunci.