Dakarun karun juyin musulunci na kasar iran IRIGC ta aike da ta’aziyar shahadar Abu obeida kakakin kungiyar izzuden qassam, kuma ta bayyana kisan gillar da Isra’ila ta yi masa a matsayin wata alama ta samun nasarar kungiyoyin gwagwarmayar falasdinu, da kuma kashe guiwar sojojin isra’ila, kuma makoma tana hannun yan gwagwarmaya.
A cikin bayanai da dakarun na IRGC ta fitar ta aike da ta’azziya da kuma murna ga dukkan alummar musulmi da kuma alummar gaza da iyalan wanda yayi shahada bayan sanar da mutuwar Abu Obeida wanda yayi shahada a cikin iyalansa tare da sauran yan gwagwarmaya guda 4.
Haka zalika IRGC ta bayyana shahadar ta sa a amatsayin wata alama ce ta nuna tsayin daka da juriya a gaban gwamnatin yan ta’adda dake kashe kana nan yara .
A jawabin nata na karshe kungiyar ta IRGC ta jaddada alkawarinta na ci gaba da wannan tafarki har sai an yanto dukkan yankunan falasdinawa da isra’ila ta mamaye a yankin falasdinu.