Masu zanga-zanga A birnin London Sun Bukaci A Saki Daraktan Asibitin Gaza

Masu rajin kare hakkin falsdinawa sun gudanar da zanga-zanga a birnin London na birtaniya, kuma ta farko a irinta ta tunawa da zagayowar ranar da

Masu rajin kare hakkin falsdinawa sun gudanar da zanga-zanga a birnin London na birtaniya, kuma ta farko a irinta ta tunawa da zagayowar ranar da sojojin Isra’ila suka kama Dr Hussam Abu safiya Daraktan Asibitin Kama lAdwan dake kudancin gaza , kuma sun yi kira da a gaggauta sakinsa bayan kwashe shakara daya a tsare.

Ci gaba da rike Dr Abu safiya yana nuna irin yadda aka nufi tsarin harkokin lafiya na gaza, adaidai lokacin sa Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban daban da aka killace da haka ya jawo damuwa sosai  game da keta dokokin jin kai na duniya da kuma ma’aikatan lafiya.

Asibitin Kamal Adwan shi na jigo na kasarshe da yake aiki a bangaren arewacin gaza a lokacin hare haren isra’ila a shekara ta 2024 , kuma an kama shugaban Asibitin ne lokacin da Asibitin yake cike da marasa lafiya kuma yake gudanar da ayyukansa cin yanayi mafi muni da killacewa.

Masu zanga-zangar sun taru ne a wajen ofishin jakadancin isra’ila dake birnin London inda suka bukaci a saki falasdinawa 9100 dake gidan yarin Isra’ila , kuma sun tuna da cika shekara guda da kama Dr Abu safiya

Ma’aikatar lafiya dake yankin Gaza ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam da su sa baki a gaggauta sakin Dr Abu safiya ,kuma ta bayyana ci gaba da rike shi a matsayin wani bangare na daukar mataki kan ma’aikatan lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted