Gwamnatin Najeriya ta ce sai da ta amince tare da bayar da izini kafin gwamnatin Amurka ta kaddamar da harin bam a kasar.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar shi ne ya bayyana haka a zantawarsa da tashar Channels, inda ya ce Shugaban Najeriya Bola Tinubu yana sane da harin kafin a kaddamar da shi.
Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da kaddamar da hari a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, da kuma jihar kwara inda ya rusa gidaje , lamarin da ya tada hankalin yan Kasar.
Da yake jawabi kan harin a safiyar Juma’a, Tuggar ya ce, “yanzu da Amurka ta fara ba mu hadin kai, za mu ci gaba da aikin ne a tare, kuma kamar yadda shugaban kasa ya nanata a jiya kafin ya amince da harin, dole aikin ya zama aikin hadin gwiwa, kuma dole ya zama babu wani addini da ake hari.
Ya ce Najeriya kasa ce mai addinai da dama, sannan ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ba ta ce amince a mata karan-tsaye a kan yancinta ba.