Rahotanni sun bayyana cewa ministan dake kula da harkokin soji na HKI Isreal Katz ya jaddada cewa gwamnatin isra’ila ba za ta taba barin yankin Gaza ba, kuma ta yi sha alwashin gina sabbin matsugunan yahudawa yan share wuri zauna a arewacin gabar yammacin kogin Jodan da hakan ya sabama yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma.
A jiya Alhamis Katz ya jaddada cewa isra’ila ba za ta janye daga Gaza ba kuma za ta kafa wani sansani mai fadi a kewayen Yankin, A lokacin da ake bukatar isra’ila ta janye baki daya daga yankin Gaza a karkashin shirin tsagaita wuta na shugaban Amurka Donals Trump.
Isra’ila ta kaddamar da yakin kare dangi ne kan gaza a watan oktoban shekara ta 2023 inda ta kashe sama da falasdinawa 70,000 kafin a kawo karshen yakin a watan oktoban da ya gabata bayan yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin bangarorin biyu.
A watan yulin shekara ta 2024 babbar kotun duniya mai hukumta laifukan yaki ICJ Ta fitar da hukumci harmata ci gaba da mamaye yankunan falasdinawa da take yi, kuma ta yi kira gareta data kwashe dukkan matsugunnan da ta gina a gabar yammacin kogin Jodan da kuma Gabashin Birnin Qudus.