Majiyar dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato IRAGC ta bada labarin cewa sun kwace wani jirnin ruwa na kasashen waje dauke da man fetur kimani lita miliyon 4 yana kokarin ficea daga kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar tana cewa, kasar Iran tana fama da satar man fetur daga kasar saboda fadin kasar da kuma bata garin da suke taimaka masu fasa korin makamashin zuwa kasashen waje.
Majiyar ta bayyana cewa an kama jirgin, sannan an kama tare da shi wadanda suke ciki, wadanda dukkaninsu yan kasashen waje gaba dayansu, ta kuma mikasu ga ma’aikatar sharia don bincike da kuma hukunta su.
Har’ila yau binciken zai hada da gano wadanda suka taimaka masu wajen satar man fetur lita miliyon 4 da suka yi kokarin fita da su daga kasar, saboda magance matsalar daga asalai. Satar man fetur daga kasar Iran dai yana gurgunta tattalin arzikin kasar ya kuma hana kasar kudaden da yakamata da samu don yiwa mutane aiki.