Najeriya ta ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda

Gwamnatin Najeriya ta ayyana masu garkuwa da mutane da kungiyoyi masu daukar makamai a matsayin ’yan ta’adda. An dau wannan matakin ne a wani sabon

Gwamnatin Najeriya ta ayyana masu garkuwa da mutane da kungiyoyi masu daukar makamai a matsayin ’yan ta’adda.

An dau wannan matakin ne a wani sabon mataki mai manufar kara tsaurara yaki da sace-sacen mutane da hare-hare da kuma tashin hankali musamman a yankunan karkara.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na karshen shekara da aka gudanar a Abuja, inda ya ce matakin ya kawo karshen rudani kan yadda ake kallon irin wadannan laifuka.

Ya ce daga yanzu duk wanda ya sace mutane ko kuma ya kai hari kan manoma ko ya tsoratar da al’umma, za a dauke shi a matsayin dan ta’adda.

Ministan ya kara da cewa “Sabon tsarin zai karfafa musayar bayanan sirri da hadin gwiwar hukumomin tsaro, lamarin da zai ba su damar daukar mataki cikin gaggawa da inganci.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted