Ministan harkokin wajen kasar Venezuela Yvan Gil yayi kira ga gwamnatin kasar Amurka ta kawo karshen jibge sojoji a ruwayen yankin Carebian, da kuma takunkuman da basa bisa ka’idan da ta dorawa kasar Venezuela.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gil yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa, ayukan sojen da Amurka ta yi a yankin ya hada zirga-zirgan danyen man fetur daga kasar Venezuela don haka ya girgiza kasuwannin man fetur da makamashi a duniya.
Ministan ya sake nanata cewa, kasar Venezuela tana bukatar Amurka ta kawo karshen killace kasarsa da kashe masu kwale-kwale a yankin da kuma karshen hana zirga-zirgan jiragen dakon man fetur a yankin.
Yace killace kasar Venezuela zai cutar da kasashen Amurka ta kudu da kasashen yankinCarabia da kuma matsalolin a kasuwannin makamashi a duniya. Minista Gil yana fadar haka ne bayan da sojojin Amurka a yankin sun kwace jiragen dakon mai na Venezuwa guda biyu, sannan tana kokarin kwace na ukku. Kafin haka Amurka tana zargin shugaba Madoro na kasar Venezuela da shugabantar kungiyoyi masu safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar Amurka, wanda mafi yawan masana suna ganin ba gaskiya ne. Sannan ya ce kasar ta kwace kayakin aikin hakar man fetur na kamfanonin Amurka da suka taba aiki a kasar a shekarun baya.