Kakakin gwamnatin kasar Iran Fatemeh Mohajerani a wani taron yan jirida da ta kira ta bayyana cewa gwamnatin kasar tana ci gaba da kyautata dangantakarta da kasashe makobta sannan tana sanya ido a kan dukkan abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya ta kudu sai kuma kufarta a bude take don na tattaunawa mai ma’a da ko wacce kasa wacce tane nufin hakan.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto Mohajerani tana fadar haka a safiyar yau talata a taron yan jarida a garin Shazand na lardin Arak inda take ziyarar aiki.
Mohajerani ta bayyana Irin halin da tattalin arzikin kasar yake ciki, ta kuma kara da cewa shugaba masoud Pezeshkiyan, a ziyarar da ya kai kasashen Kazakhistan da kuma Turkmeneistan an rattaba hannu kan yarjeniyoyi 14.
Ta ce gwamnatin kasar ta yi amini da rawar da bangaren masu zuba jari na cikin gida, kuma ta dogara da su a bangarori masu yawa don kawo ci gaban kasar. Tace gwamnati a shirye take ta tallafawa kamfanoni masu zaman kansu don bunkasa tattalin narzikin kasar kuma zata cire dukkan matsalolin da suke hana ci gaban kasa da bunkasar tattalin arziki.
Kakakin gwamnatin JMI ta kammala da cewa, dangane da matsalolin tsaro a yankin makiya musamman HKI tana kokarin ganin yankin Asiya ta kudu bai zauna lafiya ba, saboda hana ci gaban tattalina arziki da kuma siyasa. Amma gwamnatin Iran a shirye take ta fuskanci dukkan wani halin da za’a shiga ciki a yankin kuma ba zata taba amincewa harkoki su tsaya saboda rigingimun da ke faruwa a yankin ba. Ta ce Iran tana sanya ido a kan abubuwan da HKI take yi a kasar Lebanon.