Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Eidin Noruz Ga Kasashe Makwabta

Amir Abdallahiyan ministan harkokin wajen kasa iran ya aikeda sakonni mabanbanta ga takwararonsa na kasashen Azarbaikan, Uzbakistan ,Afghanistan, Pakistan, Tajikisan,Turkmenistan Turkiya, Iraki, Krygystan ,Kazakhstan da

Amir Abdallahiyan ministan harkokin wajen kasa iran ya aikeda sakonni mabanbanta ga takwararonsa na kasashen Azarbaikan, Uzbakistan ,Afghanistan, Pakistan, Tajikisan,Turkmenistan Turkiya, Iraki, Krygystan ,Kazakhstan da kuma Indiya na murnar shiga sabuwar shekara hijira shamsiya da bikin Eidin Norooz.

A jiya laraba 20ga watan maris ne aka fara bukukuwan shiga sabuwar shekara wato shekara ta 1403  hijita shamsiya a kasar iran da ma sauran kasashen makwabta da suka kada alaadu iri daya, ya fadi a sakon taya murnar cewa Eidin Nowroz  Edi ne na alada da tsohuwar wayewa da aka gada a tsawon shekaru dubbai da suka gabata da ya zama wani abu da kasashen suka yi tarayya akai

Haka zalika ya nuna cewa Alummar iran da gwamnati iran suna damuwa matuka da manufofin siyasar da suka shafi makwabtaka da juna domin zurfafa zumunci da hadin gwiwa don cin gajiyar juna, Ya bayyana fatan cewa, za a bi hanyar, sakamakon muradun kasashe da shugabannin kasashen yankin, da kuma shirya fage na ci gaba, da wadata, da tsaron yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments