Iran: Jagora Ya Ce, Kawancin Masu Gwagwarmaya A Asia Ta Kudu Sun Wargaza Shirin Amurka A Yankin

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya yabawa dakaru a cikin kawancen masu gwagwarmaya a yankin Asia ta

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya yabawa dakaru a cikin kawancen masu gwagwarmaya a yankin Asia ta kudu wadanda suka hada da Gaza  Lebanon Yemen da Iraki kan wargaza manufofin Amurka da HKI a yankin Asia ta kudu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a jiya da yamma a lokacinda yake gabatar da jawabi dangane da sabuwar shekara ta Iraniyawa a nan Tehran.

Ya kuma kara da cewa shirin Amurka a yankin Asia ta kudu ya wargaje saboda turjiyan da wadan nan masu gwagwarmaya suka nuna. Kuma a halin yanzu gwamnatin Amurka ba ta da zabi in banda ficewa daga yankin Asia ta kudu.

Jagoran ya musanta zargin Amurka na cewa Iran ce take juyya yadda yake yaken suke tafiya a yankin, ya kuma kara da cewa gaskiya ne Iran tana taimaka masu, amma kuma sune suke yakar Amurka da kawayenta da kuma HKI a yankin.

A wani bangaren na jawbainsa Jagoran ya bayyana cewa babu wani mai hankali a duniya a yau mabiyin ko wani addini ko tunan sai hankalinsa ya tashi kan kisan kiyashin da HKI

Take aikatwa a Gaza.

Daga karshen Jagoran yay akin da Falasdinawa da masu goya masu baya suke fafatawa da HKI da kuma kawayenta ya bayyana matsayin masu gwagwarmaya a yankin, sannan ya nuna irin mummunan halin da HKI da kuma Amurka suke da shi kan abinda ya shafi hakkin bi’adama da kuma tausayi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments