Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin  Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin  Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su warware matsalar rashin daidaito a cikin harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe.

Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron na G 20 ya yi Ishara da gibin kasuwanci da ake da shi a tsakanin kasashen da su ka ci gaba da masu tasowa wanda ya kamata a san yadda za a magance shi.

Antonio Gutrres ya kuma ce: “Wani abu guda daya wanda zan iya bayar da tabbaci a kansa shi ne cewa ofishin babban magatakardar MDD zai yi duk abinda zai iya yi domin yin gyara a cikin rashin daidaito da rashin adalci, sannan kuma ya tabbatar da cewa kasashe masu tasowa sun sami kyakkyawan wakilci.

Sai dai kuma babban magatakardar kungiyar ta MDD ya  yi Ishara akan  yadda MDD take da iyaka da raunin samar da sauyi a cikin mihimman cibiyoyin duniya da ake da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted