Gaza: Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 57 A Cikin Sa’o’i 24 Da Suka Gabata

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata sojojin HKI sun kai falasdinawa 57 ga shahada, wanda

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata sojojin HKI sun kai falasdinawa 57 ga shahada, wanda kuma ya kawo adadin wadanda ya kawo yawan wadanda ta kashe tun fara yakin tufanul Aksa zuwa 68,216.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar na cewa sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 45 kai tsaye da makamansu daga sama kasa da kuma ruwa a yankuna daban daban na zirin gaza a yayinda gawaki 12 kuma yana daga cikin wadanda aka zakulo daga burbushin gine-gine.

Har’ila yau sun jikata wasu Falasdinawa 158 a cikin wannan lokacin. Ma’aikatar ta kara da cewa har yanzun akwai dubban gawakin Falasdinawa a karkashin gine-ginen da aka rusa ko kuma yashi a kan tituna wanda ma’aikatan jinya basu sami damar zuwa su dauko sub a.

A wani labarin kuma itatuwa zaitun kimani miliyon 1.1 sojojin HKI suka lalata a Gaza tun bayan fara yaki a Gaza a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023. Wanda ya hana falasdinawa manoma zaitun ba tare da samun yayan zaitun ba sai kadan ko kuma babu gaba daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted