Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Yin Riko Da Hakkokin Kasarta

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Tana tabbatar da yin riko da hakkokin kasarta na kare hakkin mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya Kakakin

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Tana tabbatar da yin riko da hakkokin kasarta na kare hakkin mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa, a yayin shawarwarin da aka yi a birnin New York da kuma fahimtar da mahukuntan birnin Alkahira suka yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, jami’an yammacin duniya da ke bin Amurka, sun bukaci a maido da kudurorin takunkumin da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kakaba kan Iran a shekarar 2006 zuwa 2010, to amma kasashen China da Rasha sun fito fili suna adawa da wannan gurguwar tunani tare da jaddada rashin amince da shi.

A farkon taron manema labarai na mako-mako game da ci gaban diflomasiyya, Baqa’i ya ce: “Abubuwan da suka fi muhimmanci sun shafi halin da ake ciki a Falastinu. Duk da fahimtar da bisa ga dukkan alamu ya faru a Sharm el-Sheikh, Iran ta shaida yadda ake ci gaba da kai hare-hare a Falastinu, inda ‘yan sahayoniyya suka aikata laifukan tsagaita bude wuta sama da 80, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa kusan 100. Kamar yadda mashigar Rafah take ci gaba da kasancewa a rufe, duk da alkawura da aka dauka, ba a aike da agaji zuwa Gaza ba, kuma har yanzu gwamnatin yahudawan sahayoniyya ba ta cika alkawuran da ta dauka ba, yayin da masu tabbatar da fahimtar juna ke ci gaba da yin shiru da rashin daukar mataki, wanda hakan ya kai ga goyon bayan ci gaba da aiwatar da matakan wuce gona da iri kan Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted