Iran Ta Bukaci Kasashen Kungiyar NAM Su Hada Kai Don Fuskantar Rashin Bin Doka Da Oda A Duniya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma nuna iko na bangare guda.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Araqchi yana cewa yana daga cikin manufofin kafa kungiyar NAMA tabbatar da yencin ko wace kasa a duniya. Don haka akwai bukatar nuna wannan a aikace.

Dangane da yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran a cikin watan yunin da ya gabata, Aragchi ya ce wannan babbar shaida ce rashin bin doka da oda wanda aka shen biyu suka yi, kuma har yanzun suna barazana ga kasar.

Aragchi ya tir da kasashen turai da suka maida takunkuman MDD a kan kasarsa, bayan da kuduri mai lamba 2231 ta kawo karshen yarjeniyar JCPOA dangane da shirin makamashin nukliyar kasar Iran a ranar 18 ga watan Octoban da ya gabata. Sannan ya bukaci kasashen duniya kada su mutunta takunkuman da MDD ta sake dorawa kasarsa don basa bisa ka’ida.

Dangane da kasar Falasdinu kuma Argchi ya ce nauyin kasashen da sanyawa yarjeniyar tsagaita wuta ne su tabbatar da cewa HKI ta mutunta yarjeniyar ta kasar Masar.

Daga karshe labarin ya kara da cewa ministan ya gana da tokwarorinsa na kasashen kungiyar da dama, wadanda suka hada da tokwarorinsa na kasashen Cuban,  Eduardo, Uganda da sauransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted