Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar NAM Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Venezuela

Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan baruwanmu a  taronsu karo na 19  da ke gudana a birnin Kampala na kasar Uganda a ranakun 15 da

Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan baruwanmu a  taronsu karo na 19  da ke gudana a birnin Kampala na kasar Uganda a ranakun 15 da 16 ga wannan wata na Oktoban 2025, sun bayyana matukar damuwarsu kan halin da ake ciki a yankin Caribbean, tare da tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Jamhuriyar Venezuela wajen fuskantar duk wata barazana daga waje.

Ministocin sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, inda suka nuna matukar damuwa kan yadda lamurra suka kara tabarbarewa sakamakon tura karin sojoji da kayan yaki da Amurka ta jibge a yankin, wanda hakan ke nuni karuwar barazana ta tsaro a daukacin yankin.

Haka nan kuma Ministocin sun yi nuni da muhawarar baya bayan nan da aka yi a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar 10 ga watan Oktoban 2025, wanda ya tabbatar da bukatar bin ka’idoji na Majalisar Dinkin Duniya, da dokokin kasa da kasa, da kuma Fifita hanyoyi na tattaunawa, da diflomasiyya domin warware batutuwa masu sarkakiya da ake da sabani a kansu a tsakanin kasashen duniya.

Sannan kuma sun yi gargadin cewa, daukar duk wani mataki na soji a kan kasar Venezuela, tabbas zi yi mummunan tasiri ga makomar yankin Caribbean  baki daya.

Har ila yau, a cikin bayanin nasu sun jaddada wajabcin kare hakkokin kasashe da rashin tsoma baki cikin harkokinsu na  cikin gida, tare da goyon bayan ‘yancin  Venezuela bisa  tsarin dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted