Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh

Shugaban kasar Amurka Donal trump da shugaban kasar Masar Abdulfatta Assisi ne zasu jagoranci bikin rattaba hannu kann yarjeniyar Sulhu wacce ta kawo karshen yaki

Shugaban kasar Amurka Donal trump da shugaban kasar Masar Abdulfatta Assisi ne zasu jagoranci bikin rattaba hannu kann yarjeniyar Sulhu wacce ta kawo karshen yaki da kuma kissan kiyashin da HKI ta yi a Gaza na tsawon shekaru 2, daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa ranar Alhamis 8 ga watan Octoban shekara ta 2025.

Shafin yanar gizo na labarai ArabNews ya bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gutteres da shuwagabanin kungiyoyin kasashen Larabawa da Turai zasu halittu taron na gobe litinin a sharam Sheikh na kasar Masar.

Labarin ya kara da cewa za’a gudanar da taron ne a gobe litinin, bayan azahar kuma ana saran shuwagabannin kasashe fiye da 20.

Firai ministan kasar Burtaniya Keir Starmer, na Italiya,  Giorgia Meloni da kuma  Pedro Sanchez firai ministan kasar Spain. Da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron zai sami halattan taron.

Labarin ya kamala da cewa babu tabbas kan cewa Benyamin Natanyahu Firai ministan HKI zai halarci taron saboda yadda wasu shuwagabannin da suke halattan taron suke kinsa. Hossam Badran na kungiyar Hamas yace reshen kungiyar Hamas bata cikin yarjeniyar. Za’a fara aiwatar da musayar Fursinoni a gobe litinin tsakanin bangarorin biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted