Kasashen duniya sun fara yabawa kungiyar Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump.
Qatar mai shiga tsakanin Isra’ila da Hamas a yakin Gaza ta yaba da matakin da kungiyar ta dauka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Maged al-Ansari, wanda kuma ya goyi bayan kiran da Donald Trump ya yi na tsagaita bude wuta ya ce ” Qatar na maraba da sanarwar da Hamas ta yi cewa ta amince da shirin na Shugaba Trump.”
A nata bangare Masar tana kallon wannan a matsayin “ci gaba mai kyau.” Kuma tana fatan a sakamakon haka, bangarorin biyu “za su himmatu wajen aiwatar da shirin Shugaba Trump da kuma kawo karshen yakin,” in ji ma’aikatar harkokin wajen kasar a shafin Facebook.
Ita ma Turkiyya a cikin wani sakon da ta fitar a shafin ‘’X’’, ta bayyana lamarin a matsayin wata “dama ta samar da tsagaita bude wuta nan take a Gaza da kuma kai agajin jin kai ga yankin da kuma bude hanyar samun ci gaba wajen samar da zaman lafiya mai dorewa.”
A Turai, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi bukaci sakin mutanen da ake garkuwa da su da kuma tsagaita bude wuta.
A nasa bangaren Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya bayyana amincewar Hamas da shirin na Trump a matsayin wani muhimmin ci gaba da ke ” kusanci da zaman lafiya fiye da kowane lokaci.”
Shi kuwa Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, a cewar mai magana da yawunsa, ya samu kwarin gwiwa game da matakin da Hamas ta dauka kan shirin na shugaban Amurka, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su yi amfani da wannan damar wajen kawo karshen wannan mummunan rikici a Gaza.