Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: An yi musayar saƙo kai tsaye da kuma ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka
Ministan harlolin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Sakamakon wuce gona da iri da bukatun Amurka da kasashen Turai suke da su, ya sa an kasa cimma matsaya kan batun makamashin nukiliyar Iran. Ya ce: “Iran ba za ta amince da duk wata yarjejeniya da ba ta la’akari da muradun kasarta ba, zata aiwatar da abin da muradun kasar ke bukata, kuma Iran tana da yakinin cewa: Kwamitin koli na tsaron kasarta zai yanke shawarwari masu inganci da kyau.”
Araqchi ya kara da cewa ga manema labarai a yammacin jiya Litinin a karshen ziyararsa a birnin New York: “Sun shafe mako mai cike da shagaltuwa a birnin New York, tare da ayyuka daban-daban, wani bangare na wannan ya shafi tattauna batun sake kakaba takunkumi kan Iran, kuma lokaci guda, ko da yaushe jami’an Iran suna amfani da damar da suka samu na halartar babban taron, don karfafa dangantakar da ke tsakaninta da kasashe da kuma halartar tarukan kasa da kasa, da kuma tarukan kasashen waje da dama, a wannan shekara, mun halarci taron kasa da kasa, da kuma taruka daban-daban a kasashen waje.”
Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya ce, ya gudanar da taro da kasashe fiye da 31, da ministocin harkokin wajensu. An tattauna kan batun makamashin nukiliyar Iran, tare da jaddada matsayinta, kuma an tattauna dangantakar da ke tsakanin sauran kasashe da Iran, sannan sun yanke shawarwari kan hadin gwiwar tattalin arziki, da kuma gudanar da kwamitocin hadin gwiwa, inda kowace kasa za ta dauki nata matakan.”
Iran