Kasashen Duniya Suna Yin Gargadin Cewa HKI Za Ta Kai Wa Jiragen Ruwan Ceto Na “Sumdu” Hari

Masu kula da jirgin ruwan agaji na keta killace Gaza ( Sumudu) sun sanar da samun gargadi daga kasashen duniya da dama akan cea Isra’ila

Masu kula da jirgin ruwan agaji na keta killace Gaza ( Sumudu) sun sanar da samun gargadi daga kasashen duniya da dama akan cea Isra’ila tana shirin kai musu hari.

Jiragen ruwan  dake son kawo karshen killace sun kai  50, suna kuma dauke da kayan agaji

HKI ta aike da jiragen sama marasa matuki wadanda suke yin shawagi na tsokana a samansu da kuma watsa musu wasu sanadarori masu guba.

A jiya da dare jiragen ruwan su ka  bar gabar ruwan ‘ Girka su ka shiga iyakokin ruwan kasa da kasa da zai nausa ya nufi gabar ruwan Gaza.

A gefe daya, ministan tsaron kasar Italiya  Guido Crosetto ya bayyana cewa kasarsa za ta aike da jirgin yaki na biyu wanda zai rika bin bayan jirgin ruwan na ceto.

A gefe daya, wadanda suke cikin jirgin ruwan Agaji na “Umar Mukhtar” wanda ya taso daga kasar Libya da zummar hadewa da na “Sumud” sun bayyana cewa, a jiya Laraba wasu kananan jiragen  sama marasa matuki 3 sun rika yin shawagi a samansu. Sun kuma kara da cewa har yanzu suna ci gaba da iyo a cikin ruwan domin hadewa da babban jirgin ruwan ” Sumud”.

Kwakanin kadan da su ka gabata ne dai kasar Libya ta sanar da cewa, za ta aike da jirgin sama mai saukar angulu domin ya rika yi wa jirgin na “Umar Mukhtar” rakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted