Dubban Mutanen New Zealanda Sun Fito Jerin Gwanon Goyon Bayan Falasdinawa

A birnin Auckland, babban birnin kasar New Zealanda, dubban mutane sun fito tattaki da jerin gwano don goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza kan kissan

A birnin Auckland, babban birnin kasar New Zealanda, dubban mutane sun fito tattaki da jerin gwano don goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza kan kissan kiyashin da HKI take wa mutanen gaza kimani shekaru biyu da suka gabata.

Tashar talabejin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a jiya Asabar 13 ga watan Satumba ne masu shirya jerin gwano a birnin Auckland, na kasar suka bada labarin cewa wannan shi ne tattaki mafi girma wanda aka gudanar a cikin kasar don goyon bayan al-ummar Falasdinu tun lokacin da aka fara yakin kimani shekaru biyu da suka gabata.

Wadanda suka shirya zanga zangar sun bayyana cewa mutane kimani 50,000 suka fito wannan tattakin na goyon bayan Falasdinawa a Gaza, da kuma bukatar a kawo karshen yakin sannan a kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta.

Amma jami’an tsaro wadanda suka yi wa masu tattakin rakiya sun bayyana cewa mutanen da suka fito sun kai dubu 20. Har ila yau jamian tsaron sun bayyana cewa an gudanar da jerin gwanon ba tare da watsa matsala ba, kuma ba wanda aka kama.MDD da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama a duniya sun tabbatar da cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza ko kuma kasar Falasdinu da ta mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted