Faransa : Majalisa ta yanke kauna ga firaminista Bayrou

Majalisar dokokin Faransa ta kada kuri’ar yankan kauna wadda ta kawo karshen gwamnatin Firaministan kasar Francois Bayrou. Yan majalisar dokokin kasar sun kada kuri’ar yanke

Majalisar dokokin Faransa ta kada kuri’ar yankan kauna wadda ta kawo karshen gwamnatin Firaministan kasar Francois Bayrou.

Yan majalisar dokokin kasar sun kada kuri’ar yanke masa kauna da kashi biyu cikin uku a jiya Litini.

Bayrou dai ya shafe watanni 9 kacal akan wannan kujera a matsayin Firaminista na shida karƙashin shugabancin Emmanuel Macron da ya kama aiki a shekarar 2017, wanda a halin yanzu jam’iyyarsa ke fuskantar gagarumin rikicin siyasa.

Tuni ofishin Macron ya sanar da shirinsa na nada sabon Firaminista da zai maye gurbin Bayrou nan da kwanaki masu zuwa, yayin da Bayrou ke shirin mika takardar ajiye aiki ga shugaban kasar yau Talata.

Tuni dai jam’iyyar RN ta masu tsattauran ra’ayi da kuma masu sassaucin ra’ayi a kasar suka yi kira da a shirya kuri’ar gaggawa ta zaben ‘yan majalisu domin tilastawa Macron yayi murabus.

A shekarar 2027 ne ya kammala Macron ya kamala wa’adin mulkinsa, saidai ya ce ba mastin lamar da zai tilasta masa yin murabus kamar yadda ‘yan hamayya ke bukata.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted