Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Zirin Gaza Cikin Sa’o’i 24 Kacal

Majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 na daban suka jikkata a Gaza

Majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 na daban suka jikkata a Gaza cikin sa’o’i 24

Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da yi tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ya karu zuwa shahidai 63,633, tare da jikkatan wasu 160,914.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta bayyana a cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullun cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a cewar alkalumman baya-bayan nan da ma’aikatar ta fitar a yau Talata.

Ma’aikatar lafiya ta kididdigar mutuwar Falasdinawa 12 da jikkata wasu 90 da ke jiran agaji a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin shahidan Falasdinawa da suka isa asibitoci zuwa 2,306, tare da jikkatan wasu sama da 16,929.

Majiyar ta yi nuni da cewa, adadin wadanda suka yi shahada da jikkata tun daga ranar 18 ga Maris na shekara ta 2025, ya karu zuwa 11,502, tare da jikkatan 48,900.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted