Mataimakin Babban Kwamandan “IRGC”: Makiya Sun Kasa Cimma Munanan Manufofinsu Kan Iran

Mataimakin babban kwamandan “IRGC” ya bayyana cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna yakar Iran Mataimakin

Mataimakin babban kwamandan “IRGC” ya bayyana cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna yakar Iran

Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Fadavi ya tabbatar da cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Iran. Duk da tsare-tsare masu yawa da kuma sanar da manufofinsu a baya, makiya sun kasa cimma wata manufa da suka ayyana a cikin yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan Iran, lamarin da ya tilasta musu amincewa da shan kashi ta hanyar amincewa da tsagaita bude wuta cikin hanzari.

Fadavi ya kara da cewa: Amurka duk da matsayinta na kasa mai karfin duniya da kuma dogaro da kasashe da dama a kanta, ta kasa cimma burinta na kawar da tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ko kuma raunanata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted