Babban sakataren majalisar tsaron kasa a Iran Ali Larijani, ya jaddada aniyar Tehran ta karfafa diflomasiyya tare da yin gargadin cewa tattaunawa mai ma’ana za ta iya ci gaba ne kawai idan Amurka da Turai suka amince cewa matsin lamba da barazanar yaki ba za su razana al’ummar Iran ba.
Larijani ya jaddada cewa har yanzu harkokin diflomasiyya wani makami ne na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, amma sai an gudanar da shi cikin aminci.
“Shawarata ita ce, kada Iran ta yi watsi da harkokin diflomasiyya, domin ita kanta diflomasiya kayan aiki ne,” in ji shi. Har ila yau, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, tilas ne a rike tutar tattaunawa a hannu a koda yaushe.
Larijani, ya yi gargadin cewa tattaunawar ba za ta yi nasara ba idan kasashen Yamma suka yi amfani da su a matsayin mafaka ga ayyukan nuna gaba da kiyayya.
Dangane da wannan batu, Larijani ya yi nuni da cewa kasashen yamma sun yi amfani da tsarin diflomasiyya a matsayin hanya da yaudara da dabara maimakon hanyar samar da zaman lafiya ta gaskiya.
Sannan kuma ya bayyana jan layi na Iran wanda ba za ta taba amincewa a ketare shi ba, ya ce Idan kasashen turai yaki suke nema, to sus ani cewa Iran ba za ta taba mika wuya ba.
Ya yi nuni da cewa, tuni kalamai da matakai na matsin lambar kasashen yammacin duniya a kan Iran suka zama marasa tasiri. Ya kara da cewa, “A cikin wannan yakin, su da kansu sun fahimci cewa Iraniyawa ba irin mutanen da za su mika musu wuya ba ne.”
Da aka tambaye shi game da yiwuwar Iran ta fice daga NPT idan aka kara matsin lamba a kan kasar, Larijani bai kawar da yiwuwar hakan ba. “Wannan zabe zai iya kasancewa a ko da yaushe,” in ji shi.
Ya kuma soki kokarin da Turai ke yi na farfado da tsarin da ake kira “snapback”, ko kuma tsarin dawo da takunkumai, yana mai bayyana shi a matsayin barazana da ke kawo cikas ga duk hankoron komawa kan teburin tattaunawa.
Ya ce kasashen Turai suna bayar da himma wajen hidima ga ajandar Washington. “Halayensu a bayyane suke; suna aiwatar da wani bangare na ayyukan Amurka da manufofinta.”
Larijani ya yi watsi da tsarin da kasashen turai suke bi, yana mai bayyana shi a matsayin tsari wanda yake cike da kura-kurai na shari’a da siyasa.
Ya kuma yi nuni da rashin bin ka’ida. “Idan kuna son yin amfani da tsarin dawo da takunkumai kan Iran, ba za ku iya zuwa kai tsaye ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba, domin kuwa akwai matakai da sharudda wadanda dole ne sai an bi su kafin gabatar da wannan batu, wanda kasashen turai basu yi aiki da ko daya daga cikin sharudda da tsarin ya kunsa ba.